A yau Talata, Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da ginin cibiyar fasahar kere-kere ta hukumar kula da shige da ficen Najeriya a shelkwatarta dake birnin Abuja.
Cibiyar ta kunshi bangaren kula da harkokin shige da fice na yau da kullum dana sarrafa bayanai da ofishin samar da katin tafiye-tafiye na kungiyar ecowas, ta bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma dana sarrafa bayanan cikin gida da kuma tashar samar da kilo 0.5 na lantarki daga hasken rana.
A jawabinta na bude taro, shugabar hukumar shige da ficen Najeriya, Mrs Kemi Nanna Nandap tace cibiyar fasahar kere-kere ta Bola Tinubu na iya tantance irin hadarin dake tattare da mutanen dake shigowa kasar tare da gano hanyoyin yin kaura ta barauniyar hanya da kuma sanya idanu akan iyakokin najeriya da babu jami’an dake kula dasu a yankunan masu wuyar kaiwa a fadin kasar.
Ta kara da cewa cibiyar da na’urorin dake cikinta zasu “tsayar da mizanin amfanin da fasaha wajen sanya idanu akan iyakokin kasa domin tabbatar da tsaronta.”
Dandalin Mu Tattauna