Babbar kotun birnin tarayyar Najeriya Abuja ta bada ajiyar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a gidan gyaran hali na Kuje kafin ta saurari bukatar neman belinsa.
Haka kuma kotun ta dage zamanta zuwa 29 ga watan Janairu da 27 na watan Febrairun 2025 domin cigaba da sauraron karar.
Mai Shari’a Maryam Anenih taki amincewa da bukatar neman belin da Yahaya Bello ya shigar, inda tace an gabatar da ita da wuri.
Bello ya shigar da bukatar neman belin ne a ranar 22 ga watan Nuwamban daya gabata amma sai a ranar 26 ga watan aka tsare shi sannan aka gurfanar da shi a kotu a ranar 27.
Tsohon gwamnan na fuskantar tuhuma tare da wadansu mutane 2, akan zargin halasta kudaden haram har Naira bilyan 110 da hukumar efcc mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ke yi masa.
Dandalin Mu Tattauna