Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya jaddada cewa za’a iya samun nasarar yakin da ake yi da cin hanci da rashawa ne kawai idan manyan jami’an gwamnatin suka rika bada bahasi a kan abin da suke aikatawa.
Tsohon shugaban kasar yace magance matsalar rashawa a matakin manyan shugabannin zai kafa misali ga wasu kuma zai nuna jajircewar gwamnati a kan tabbatar da gaskiya da adalci.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a daren jiya Lahadi a wata tattaunawar da wani gidan rediyo mai zaman kansa dake birnin Abeokuta fadar gwamnatin jihar Ogun yayi da shi a shirinsa mai taken: “Boiling Point Arena”.
Tattaunawar wacce wasu gidajen rediyon masu zaman kansu suka yada a birnin na Abeokuta, ta maida hankali ne akan ayyukan gwamnatin Obasanjo da kuma yadda yake kallon Najeriya a yau.
Dandalin Mu Tattauna