Ma’aikatar harkokin wajen najeriya tace har yanzu Shugaba Bola Tinubu bai nada jakadu ba.
Ma’aikatar na martani ne ga wani jerin sunaye da ake yadawa a kafafen sada zumunta na mutanen da Shugaba Tinubu ya nada a matsayin jakadun Najeriya a kasashen duniya daban-daban.
A sanarwar da ya fitar a jiya Lahadi mai rikon mukamin kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya bukaci al’umma da suyi watsi da jerin sunayen.
“Da kakkausar murya, ma’aikatar ke bayyana cewa nadin jakadu hurumi ne na shugaban kasa, kuma bai nada kowa,” a cewar Ebienfa.
A watan Satumban 2023, Tinubu ya janye dukkanin jakadun Najeriya dake aiki a kasashen duniya daban-daban.
Dandalin Mu Tattauna