Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Sanata George Akume, yace kamata yayi ‘yan arewacin Najeriya dake kwadayin shugabancin kasar a 2027 su hakura zuwa 2031.
Akume ya kuma baiwa masu sha’awar shugabancin Najeriya su jira zuwa 2031, lokacin da shugaban dake kai, Bola Tinubu, ya kammala wa’adinsa na 2.
“A kyale Shugaba Tinubu, dan kudancin Najeriya, ya yi wa’adi na 2, abin da ke nufin ya kamata masu sha’awar neman mukamin daga arewa su saurara har sai bayan 2031.
“Idan har Allah ya kaddara cewa Alhaji Atiku Abubakar zai shugabanci Najeriya, koda yana da shekaru 90, zai iya samu, sai dai kamata ya yi shi da sauran ‘yan arewa dake sha’awar kujerar, su jira sai bayan 2027.”
Ya kuma roki ‘yan Najeriya dasu kyale kudurorin nan su bi matakan majalisar da ake bukata, inda yace akwai alherin dake cikin kudurorin ga ‘yan Najeriya.
Akume, wanda ya bada shawarwarin a cikin shirin siyarar tashar talabijin na tvc na ranar lahadi ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar shugaba bai rasa soyayyar ‘yan Najeriya ba saboda kudurorin gyaran haraji da muhimman sauye-sauyen tattalin arzikin daya aiwatar a watanni 17 din da suka gabata.
Ya kuma ba da kariya ta musamman ga kudurorin gyaran dokar haraji inda yace akwai tanade-tanade masu kyau da zasu fidda kasar nan daga kangi matukar majalisar kasa ta nazarcesu tare da zartar dasu.
Dandalin Mu Tattauna