Wannan ne babban abun da Tinubu ya ce ya amince da shi nan take daga abun da gwamnatin Buhari ta gadar ma sa.
Shugaban wanda ya sha rantsuwa bisa tanadin tsarin mulki; ya ce tallafin ba shi da wani amfanin da ya wuce azurta 'yan jari hujja.
Duk da lalle hakan zai jefa talakawa cikin karin kunci; Tinubu ya kare matakin da cewa za a tura tallafin wani sashen da zai fi taimakon al'umma.
Tinubu ya ce duk 'yan Najeriya nasa ne kuma ya mika tayi ga sauran 'yan siyasa su zo a tafi tare a tsira tare.
Kazalika ya ce zai daidaita canjin Naira, samar da tsaro da ba wa mata da matasa dama.
Tun gabanin nan tsohon shugaba Buhari ya yi bankwana ya kama hanyar Daura wasu na juyayi wasu na Allah raka taki gona.
Shugaban magoya bayan Tinubu Kailani Muhammad ya ce bai yi wani juyayi ba.
Hannatu Musawa na daga matan da su ka nuna kwarin gwiwar nasara a sabuwar gwamnatin.
Ko me za a ce yanzu, ba za a dora da manyan bayanai ba, sai an ga kamun ludayin nada mukaman gwamnatin Tinunu.
Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya: