Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nemi Hallaka Ni Sabili Da Toshe Kafar Satar Kudi A Najeriya: Ngozi Okonjo-Iweala


Ngozi Okonja-Iweala.
Ngozi Okonja-Iweala.

Darektar Kungiyar Cinikayya ta Dunitya WTO Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa an yi kokarin hallakata lokacin tana Ministar kudi a Najeriya sabili da ta yi kokarin toshe hanyoyin da Najeriya ke asarar kudi.

A hirarta da Ngozi Okonjo-Iweala wata fitattar cibiya a Amurka da ake kira Atlantic Council, darektar hukumar WTO ta ce daukar wannan matakin ya kai ga ceto kasar daga asarar kudin da ya kai dala biliyan uku da miliyan dari shida da ake biyan ma’aikatan boge da kuma ‘yan damfara.

Tsohuwar Ministar kudin wadda a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ta tattauna da kasashen waje masu ruwa da tsaki a fannin bada basusuka da ya kai aka zaftare bashin da ake bin Najeriya na dala biliyan talatin, da kashi sittin cikin dari.

Ngozi Okonjo-Iweala, da Ministar Cinikayya na kasar Faransa Franck Riester
Ngozi Okonjo-Iweala, da Ministar Cinikayya na kasar Faransa Franck Riester

Ngozi Okonjo-Iweala wadda ta yi aiki a matsayin Ministar Kudi karkashin gwamnatocin Shugaba Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan ta ce bayan ta samu nasarar tsaida yarjejeniyar da ta kai ga zaftare bashin da ake bin Najeriya da kuma rage kudin ruwan da kasar ke biya kan bashin, matakin da ya taimaka ya daga karfin tattalin arzikin kasar, ta maida hankali wajen yaki da rashawa da barnar kudi a lokacin da ta yi aiki karkashin mulkin Goodluck Jonathan.

Karin bayani akan: Ngozi Okonjo-Iweala, Goodluck Jonathan, WTO, Bankin Duniy, Atlantic Council, Nigeria, da Najeriya.

Darektar WTO ta ce a karkashin mulkin Goodluck Jonathan ne aka nemi hallaka ta aka kuma yi garkuwa da mahaifiyarta. Ta bayyana cewa a lokacin ta gano, gwamnati na asarar biliyoyin dala wajen biyan barayin biro da suke satar kudi ta wajen shigar da sunayen ma’aikatan boge, da kuma wadanda ke damfarar gwamnatin ta wajen kara yawan kudin da ake biya kan sassaucin man fetir.

DireKta Janar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala
DireKta Janar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala

Banda manyan mukamai da Ngozi Okonjo-Iweala ta rike da cibiyoyin kasashen duniya da ya hada da babbar darekta a babban Bankin Duniya, ta yi fice a matsayin mace da ta rike mukamin Ministar Kudi har sau biyu a Najeriya karkashin gwamnatoci dabam dabam ta kuma rike mukamin Ministar harkokin kasashen ketare. A shekara ta 2015 Cibiyar Euromoney ta ayyana Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Ministar kudi da ta fi kowanne fice a duniya.

okonjo-iweala-ta-fara-aiki-a-matsayin-shugabar-hukumar-kasuwanci-ta-duniya

kungiyar-kasuwanci-ta-duniya-na-bukatar-sabon-salon-gudanarwa-dr-ngozi

zaben-ngozi-okonjo-iweala-afurka-ta-samu-mai-share-mata-hawaye

Ngozi Okonjo-Iweala A Matsayin Shugabar Kungiyar WTO

Ngozi Okonjo-Iweala A Matsayin Shugabar Kungiyar WTO
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG