Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Aljeriya Ta Isa Nijar Domin Karfafa Dangantaka Tsakanin Kasashen


Lokacin da tawagar ‘yan Algeria ta isa Nijar
Lokacin da tawagar ‘yan Algeria ta isa Nijar

Wata tawaga karkashin ma'aikatar ministan harkokin wajen kasar Aljeriya na ziyarar aiki a Nijar inda tare da hukumomin jihar Agadas dake arewacin Nijar suka tattauna kan wasu mahinman batutuwa  da dama ta bangaren tattalin arziki, kiwon lafiya , gina makarantu da dai saurensu

AGADEZ, NIGER - Tawagar ta ziyarci mahimman wuraren da aka kebe domin gina jami’ar Musulunci da kuma wata babbar asibiti mai kula da masu fama da cutar koda da tashar samarda wutar lantarki mai aiki da hasken rana da kuma wasu ayyuka na raya kasa.

“Yan Nijar sun tarbi tawagar Algeria
“Yan Nijar sun tarbi tawagar Algeria

Yayin wannan ziyarar, tawagar ta kuma ziyaraci wasu ayyukan da kasar Aljeriya ta soma domin anfanin arewacin Nijar.

Kasar Aljeriya dai tun asali tana da kima a idanuwan al’ummar Nijar sakamakon manyan tsare-tsaren kasar da ta gudanar a kasar ta Nijar.

Shugaban mulkin soja Nijar da wani daga tawagar Algeria
Shugaban mulkin soja Nijar da wani daga tawagar Algeria
Ziyarar tawagar Algeria zuwa Nijar
Ziyarar tawagar Algeria zuwa Nijar

Masana sun bayyana fatan ganin kasashen biyu sun karfafa dangantaka ta fuskar siyasa da tattalin arziki ta yadda ‘yan kasar Nijar zasu rika gani a kasa aduk wata hulda da gwamnatin mulkin sojan Nijar zata yi tsakanin kasa da kasa musamman kasar Aljeriya da ke zaman babbar kawa ga kasar Nijar wacce suka raba iyaka mai yawa a arewacin kasar.

‘Yan tawagar Algeria da suka kai ziyara Nijar
‘Yan tawagar Algeria da suka kai ziyara Nijar

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud

Karfafa Dangantaka Tsakanin Jamhuriyar Nijar Da Aljeriya .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG