A jiya Talata aka kawo karshen fafatawar neman gurbi a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 2025, inda dukkanin tawagogi 24 da zasu kece raini a gasar suka bayyana.
Yayin da wasu tawagofin suka samu cancantar shiga gasar tunda fari, saura irinsu Jamhuriyar Benin sun samu nasu tikitin shiga gasar ne a kurarren lokaci.
Gasar wacce zata gudana cikin watan Disamba mai zuwa a kasar Morocco, inda mai masaukin bakin ta samu gurbin shiga gasar kai tsaye.
Sai dai wasu daga cikin manyan tawagogi irinsu kasar Ghana ba zasu samu shiga gasar ba wacce ake sa ran manyan kungiyoyi irinsu Najeriya da Masar da Afrika ta Kudu da Tunsia, da masu rike da kofin a halin yanzu Ivory Coast na cikin kasashen da zasu fafata a gasar ta kungiyoyi 24.
Ga cikakken jerin sunayen tawagogin da suka samu nasarar shiga gasar AFCON ta 2025 a nan kasa:
1. Algeriya
2. Angola
3. Jamhuriyar Benin
4. Botswana
5. Burkina Faso
6. Kamaru
7. Comoros
8. Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo
9. Masar
10. Equatorial Guinea
11. Gabon
12. Ivory Coast
13. Mali
14. Mozambique
15. Najeriya
16. Senegal
17. Afirka taKudu
18. Sudan
19. Tanzaniya
20. Tunisiya
21. Uganda
22. Zambiya
23. Zimbabwe
24. Moroko
Dandalin Mu Tattauna