Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba A Tsangwamar ‘Yan Najeriya A Libya – Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya


Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce babu kamshin gaskiya a labarin.

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta musanta rahotanni da ke nuni da cewa ana tsangwamar ‘yan kasarta a Libya biyo bayan hukuncin da hukumar kwallon kafar Afirka ta CAF ta yanke.

“Ma’aikatar harkokin waje, na so ta sanar da cewa, ya zuwa lokacin fitar da wannan sanarwa, babu wani dan Najeriya da ya fuskanci tsangwama a dalilin hukuncin CAF, domin suna can suna gudanar da harkokinsu.” Sanarwar dauke da sa hannun Kakakin ma’aikatar Ambasada Eche Abu-Obe ta ce.

A ranar 26 ga watan Oktoba CAF ta ba Najeriya maki uku bayan da ta ayyana cewa Libya ta karya doka ta 31 karkashin ka’idojin hukumar.

‘Yan wasan Najeriya sun fasa karawa da Libya a wasa na biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka na AFCON bayan da aka ajiye su a wani filin tashin jirage tsawon sa’o’i 16 a kasar ta Libya.

Hakan ya sa hukumomin kwallon kafar Najeriya suka shigar da kara bayan janyewa daga wasan inda daga karshe CAF ta samu Libya da karya dokar hukumar.

Libya ta ce za ta kalubalanci hukuncin.

Sai dai wasu rahotanni na nuni da cewa an fara tsangwamar ‘yan Najeriya a kasar ta Libya wacce ke fama da yake-yake bayan wannan hukunci na CAF.

Amma ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta ce babu kamshin gaskiya a labarin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG