Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar Za Ta Kafa Wani Yanki Akan Iyakar Gaza Wanda Zai Iya Zama Mafaka Ga Falasdinawa - Majiyoyi


Falasdinawa a kusa da kan Iyakar Gaza da Egypt, Fabrairu 16, 2024
Falasdinawa a kusa da kan Iyakar Gaza da Egypt, Fabrairu 16, 2024

Masar na shirin shirya wani yanki a kan iyakar Gaza wanda zai iya daukar Falasdinawa idan har hare-haren Isra'ila a kan Rafah ya yi sanadin 'yan gudun hijirar zuwa kan iyaka, in ji majiyoyi hudu, a wani mataki da suka bayyana a matsayin wani yunkuri na gaggawa da birnin Alkahira ke shiryawa.

WASHINGTON, D. C. - Masar, wacce ta musanta yin irin wannan shiri, ta sha nuna fargaba kan yiwuwar mumunar harin da Isra'ila ke kaiwa Gaza ka iya korar Falasdinawa zuwa Sinai, abin da Alkahira ta ce ba zai zama abin amincewa ba kwata-kwata, wanda yake gargadin kasashen Larabawa irin su Jordan.

Amurka ta sha nanata cewa za ta yi adawa da korar Falasdinawa daga Gaza.

Daya daga cikin majiyoyin ta ce Egypt na da kwarin gwiwar yin shawarwarin tsagaita wuta da za a iya kaucewa irin wannan yanayin, amma tana kafa yankin a kan iyaka a matsayin na wucin gadi da yin taka tsantsan.

Wasu majiyoyin tsaro uku sun ce Egypt ta fara shirya wani yanki na hamada ne mai dauke da wasu muhimman abubuwan da za a iya amfani da su wajen fakewar Falasdinawan, suna jaddada cewa hakan wani mataki ne na gaggawa.

Majiyoyin da Reuters ta zanta da su akan wannan labari sun ki a bayyana sunansu saboda azancin lamarin.

Isra'ila ta ce za ta kai farmaki don kakkabe sansanin Hamas na karshe a Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan 1 suka nemi mafaka daga mummunan harin da ta kai kan Gaza.

Isra'ila ta kuma ce sojojinta na shirin kwashe fararen hula daga Rafah zuwa wasu yankunan zirin Gaza.

Ya kira wannan yanayin "wani irin mafarki na Egypt mai ban tsoro."

Egypt ta nuna adawarta da korar Falasdinawa daga Gaza a matsayin wani bangare na kin amincewa da duk wani maimaicin "Nakba," ko " bala'i," lokacin da Falasdinawa kusan 700,000 suka fice ko kuma aka tilasta musu barin gidajensu a yakin da ya gudana yayin kirkiran kasar Isra'ila a 1948.

Majiyar farko ta ce an fara gina sansanin ne kwanaki uku ko hudu da suka gabata kuma zai ba da matsuguni na wucin gadi a kowane yanayi na mutanen da ke ketare iyaka "har sai an cimma matsaya."

Da majiyoyin suka tambaye shi game da asusun, Shugaban hukumar yada labaran kasar Masar ya ce: "Wannan ba shi da tushe a kan gaskiya, 'yan uwanmu Falasdinu da kasar Masar duk sun ce, babu wani shiri na yin hakan."

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG