Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashe Tashen Hankalin Kungiyoyin Daba Ya Daidaita Sama Da Yara 300,000 A Kasar Haiti


Haiti
Haiti

Karin tashe tashen hankulla ya kara Kamari ne a karshen watan Fabrairu, bayan dimbin jerin shiryayyun hare hare kan muhimman gine ginen gwamnati da sannu a hankali ya kai ga Priministan kasar Ariel Henry ya tattara shugabancin kasar ya ajiye a watan Apirilu.

Tashe tashen hankalin kungiyoyin daba ya daidaita sama da yara 300,000 a kasar Haiti, tun a watan Maris, a cewar asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya a jiya Talata, a yayin da kasar ta Karebiyan ke fadi tashin shawo kan kashe- kashe da satar mutane da ya addabi kasar.

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya yace, yara ne sama da rabin adadin kusan mutane 580,000 da su ka rasa muhallan su, a cikin watanni hudu da su ka wuce.

Tashe tashen hankulla ya kara kamari ne a karshen watan Fabrairu, bayan dimbin jerin shiryayyun hare hare kan muhimman gine ginen gwamnati da sannu a hankali ya kai ga Priministan kasar Ariel Henry ya tattara shugabancin kasar ya ajiye a watan Apirilu.

Babbar daraktar asusun yara ta Majalisar Dinkin Duniya, Catherine Russel, ta fadi cikin wata sanarwa cewa, babban bala’in jinkai da suka rika gani yayi munin gaske a kan yara. Tace, yaran da aka daidaita na cikin tsananin bukatar muhalli mai tsaro da kariya, da karin tallafi da taimakon kudi daga al’ummomin duniya.

A yanzu kungiyoyin 'yan daba ke rike da akalla kashi tamanin da ga cikin dari na babban birnin kasar Port-au-Prince, da manyan hanyoyin shiga da fita daga birnin, inda aka kashe ko raunata mutane sama da 2, 500 a sassan kasar a farkon watanni uku na shekarar 2024 cewar majalisar dinkin duniya.

Yara da dama na rayuwa ne a matsatstsun wuraren da aka sama musu, da ya hada da makarantu da ke cikin mummunan yanayin rashin tsabta, da hakan ya jefa su cikin hadarin kamuwa da cututtuka. Haka zalika rufe makarantu ya haifar da karuwar yara da ke jingine karatun su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG