Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewar tana samun karin tallafi daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) a yayin da take kokarin yakar annobar kwalara a gidan yarin Kirikiri.
Sanarwar da Kwamishinan Lafiyar jihar, Akin Abayomi, ya fitar a ranar Lahadi na cewa an samu mutum 25 da suka kamu da annobar kwalara a gidan yarin kirikiri, inda ya kara da cewar an dauki matakan kiwon lafiya dana tsaftar muhalli cikin nasara.
“Mun samarwa gidan yarin na Kirikiri da ruwan karawa majinyata da magungunan yaki da annobar da sauran kayayyakin kiwon lafiya. Har ila yau, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ba da gudunmowar allurai dubu 10 ga asibitin gidan yarin da kayayyakin rigakafi na kimanin fursunoni dubu 3 da 200 idan ana bukata.
"Kuma nan take an yi gyara akan batun samarda ruwan sha da tsaftar muhalli kuma ana cigaba da sanya idanu akan sauran gidajen yarin dake jihar”. A cewar kwamishinan,
Gwamnatin jihar Legas ta kuma ba da sanarwar samun gagarumar raguwar yawan mutanen da ke kamuwa da kwalarar a kowace rana, sabanin irin rimin da annobar ta yi a makonni biyu da suka gabata.
Sai dai gwamnatin ta amince da shaidar ci gaba da samun yaduwar cutar a unguwannin talakawa, kasancewar ana ci gaba da kai mutanen da suka kamu da annobar zuwa asibitoci a ko’ina a fadin jihar.
Da yake jawabi akan tushen barkewar annobar a makonni biyu da suka gabata, kwamishinan lafiyar na jihar Legas ya bayyana cewar sun gano tana da alaka da ababen sha da ake sayarwa a gefen titi da gurbataccen ruwan sha.
Dandalin Mu Tattauna