Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Shugabannin Manyan Kasashen Duniya a Jamus


Shugabannin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.
Shugabannin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.

A yau Juma’a shugabannin kasashe masu karfin arziki na G20 a duniya ke haduwa a birnin Hamburg na kasar Jamus, domin gudanar da taron kwanaki biyu kan nemo bakin zaren warware wasu matsaloli.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, na karbar bakuncin shugabannin manyan kasashen duniya da suka fi karfin tattalin arziki wadanda ake wa lakabi da G20.

Taron zai yi dubi ne kan yadda za a warware matsaloloin da suka sha musu kai, kamar na hadahadar kasuwancin da yaki da ta'addanci da sauyin yanayi.

Ko da yake har yanzu babu wata matsaya kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi da kuma cinikayya.

Babu daidaito tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da sauran shugabannin manyan kasashen duniya, tun lokacin da ya cire Amurka daga yarjejeniyar da aka kulla a Paris don tukarar sauyin yanayi.

Trump ya ce yana shirin kakaba haraji ga duk karafunan da za a shigo da su Amurka, wanda hakan ke zama wata babbar barazana wajen kare kamfanonin Amurka, wanda hakan ya ta da hankalin shugabannin na G20.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG