Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Hanci na Kin Kari Ya Koma Tsakanin 'Yansanda da 'Yansanda


Rundunar 'Yansandan Najeriya
Rundunar 'Yansandan Najeriya
A wata fira da wakilin Muryar Amurka Ladan Ibrahim Ayawa ya yi da wani dansanda da ya kira Tanko domin kare sunasa sun zanta kan abubuwa da dama da suka shafi yadda 'yansandan Najeriya suka yi kamarin suna wurin cin hanci rashawa da murdiya.

Dansanda Tanko yace sabili da wayar tafi da gidanka mai daukan hoto yawancin 'yansanda na jin tsoron karban na goro a hanya domin wasu sun soma daukan hotonsu suna aikawa manyansu lamarin da wani zibin kan kaiga korar mai laifin daga aiki. Sanadiyar hakan masu wayo cikinsu su kan yi takatsantsan kafin su karbi abu a hanya.

A cigaba da firar tasu Dansanda Tanko yace ai yanzu cin hanci na kin kari ya koma tsakanin 'yansanda da 'yansanda. Misali idan kana son ka je yin kwas domin ka samu ci gaba to sai ka biya manya da zasu zabeka abun da ya kama daga nera dubu goma sha biyar ko ma fiye. A wurin kwas din idan har ka samu ka je to can ma sai ka miya manyan kafin a ce ka ci. Bata tsaya nan ba domin kafin a sa sunanka cikin jerin sunayen wadanda za'a duba ko sun cancanta a kara masu girma sai ka biya.

Bayan mutum ya samu cigaban sai kuma a zo batun sa suna cikin sabbin wadanda suka samu karin girma. Nan ma sai ka biya mai buga sunayen kudi nera uku ko fiyeda hakan. Idan baka biya ba zai jire sunaka babu wuya kuma sunan wani ya maye gurbin naka koda wannanan din bai yi kwas da kai ka yi ba.

Dansanda Tanko ya hakikance cewa kowane kwamanda yana sane da abubuwan dake faruwa a karkashinsa. Yace manyan kashe mu raba su keyi. Yace lamarin cin hanci tsakanin 'yansanda har ma ya yi masu katutu.

Ga firar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:12:14 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG