Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bobrisky: Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Zargin Almundahanar Da Ake Yiwa EFCC, NCS


Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

A yau Alhamis, Majalisar Wakilai, ta amince da kudirin bincikar zarge-zargen almundahanar da wani mawallafi a kafafen sada zumunta, Martins Otse da aka fi sani da Verydarkman ke yiwa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya da takwararta ta kula da Gidajen Gyaran Hali na Najeriya (NCS).

Kudirin majalisar na zuwa ne bayan amincewa da wata bukata mai matukar mahimmanci ga al’umma da dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Ekpene/Essien Udim/Obot daga jihar Akwa Ibom, Patrick Umoh ya gabatar.

A jawabinsa Umoh ya bayyana damuwa game da karade shafukan sada zumuntar da abubawan da Verydarkman ya wallafa a kan hukumomin EFCC da NCS.

Bayan amincewa da kudirin, Kakakin Majalisar Tajudeen Abbas wanda ya jagoranci zaman, ya mika batun zuwa ga kwamitocin majalisar akan laifuffuka kuma da gidajen gyaran hali.

Ana sa ran kwamitocin su dawowa majalisar da rahotonsu cikin makonni 3 domin daukar mataki na gaba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG