Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Iya Murkushe Matsalar Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya – EFCC


Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede
Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede

Olukoyede ya yi wadannan kalaman ne a Abuja a ranar Talata, 1 ga Oktoba, 2024, a cikin sakon bikin ranar ‘yancin kai ga ‘yan Najeriya.

Shugaban Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Ola Olukoyede, ya ce Najeriya za ta iya magance matsalar cin hanci da rashawa baki daya idan aka jajirce.

Yayin bikin cikar kasar shekaru 64 da samun ‘yancin kai, Olukoyede ya ce akwai bukatar kowa ya sabunta aniyarsa ta yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda hukumar ta fada a cikin wata sanawar da ta fitar a ranar Talata.

Matsalar cin hanci da rashawa na daga cikin dumbin matsalolin da ke addabar Najeriya wacce ta fi yawan al’uma a nahiyar Afirka.

Olukoyede ya yi wannan kiran ne a Abuja ranar Talata, 1 ga Oktoba, 2024, a cikin sakon bikin ranar ‘yancin kai ga ‘yan Najeriya.

A cewarsa, EFCC ta himmatu sosai wajen tabbatar da cewa Najeriya ta zama kasa da ta kawar da wannan matsala kuma ya bukaci duk wani dan Najeriya da ya kara hada kai da hukumar wajen magance ta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG