Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tantancewa: Mike Pompeo Ya Sha Da Kyar A Gaban Wani Kwamiti


Mike Pompeo
Mike Pompeo

Biyo bayan kuri'ar goyon bayan da Pompeo ya samu, ana kyautata zaton zai sami amincewar duk 'yan majalisar dattawan Amurka.

Mike Pompeo, mutumen da shugaba Donald Trump ya mika sunansa don tabattar da shi a matsayin sabon sakatarensa na harakokin waje, ya tsallake rijiya da baya wajen kaucewa yin wani abin kunyar da ba wanda ya taba fuskanta a gaban ‘yan kwamitin Majalisar dattawa, bayanda ya sami goyon bayan daya daga cikin ‘yan kwamitin, Rand Paul na jihar Kentucky, wanda ya chanja ra’ayinsa gameda jefa mish kuri’ar goyon baya.

Pompeo ne zabin zama sakataren harkokin wajen Amurka karon farko a zamanin nan wanda ya gaza samun amincewa daga kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattawan, yayinda Paul da wasu ‘yan jam’iyyar Democrat su 10 a cikin kwamitin suka sanar da cewa ba zasu amince da shi ba.

Amma a lokacin da kwamitin ke shirin jefa kuri’a, Paul yayi wata sanarwar ta bam mamaki, inda yace, “Na canza ra’ayina. Na yanke shawarar zan jefa kuri’ar goyon bayan Mike Pompeo.” Dan majalisar yayi bayanin cewa ya sami kwarin guywa daga ganawarsa da Mike Pompeo da shugaba Trump, akan abubuwan da suka faru a yakin Iraqi da kuma wasu batutuwan dake da muhimmanci gareshi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG