Tsohon Shugaban Amurka, George HW Bush na samun sauki sosai a asibiti bayan da ya kamu da wata cuta ta jini mai barazana ga rayuwarsa, a cewar wani mai magana da yawun iyalin tsohon shugaban.
An kwantar da dattijo Bush mai shekaru 93 da haihuwa a asibitin da ake kira Houston Methodist ranar Lahadi da safe kuma an ajiye shi a fannin masu bukatar kulawa sosai.
Tsohon shugaban ya yi mulki wa’adi daya, daga 1989 zuwa 1993. Yanzu yana amfani da keken guragu da kuma wani keken mai amfani da lantarki don zagayawa, bayan da ya kamu da cutar da ake kira Parkinson mai sa makyarkyatar jiki. An sha kwantar da shi asibiti a ‘yan shekarun da suka gabata saboda matsalolin da suka shafi numfashi, ciki harda cutar namoniya.
Facebook Forum