Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kyamar Musulmai A Amurka Ta Karu Da Kashi 15 Daga Shkarar 2017


Musulman Amurka
Musulman Amurka

Tun daga lokacin da shugaban Amurka na yanzu ya kama mulki kyamar da ake yiwa musulmi a nan Amurka ya karu da kashi 15 kamar yadda kungiyar dake kare muradun musulman kasar ta bayyana


Laifukan tsana ko kyama da ake auna Musulmi a Amurka ya karu zuwa kashi 15 cikin dari a shekarar 2017, shekaru biyu a jere da ake samu karuwar haka, a cewar wani nazari da aka bayyanar da sakamakonsa a jiya Litinin da wata kungniyar fafutukar kare Musulmi a Amurka da ake kira Council on American-Islamic Relations wato CAIR atakaice.


Kungiyar ta sami rahotanni kan kyama ko tsana 300 da aka auna kan Musulmi a Amurka a bara, tun daga dukar wani Musulmi bisa zarginsa cewa shi dan ta’adda ne a gundumar Bronx a birnin New York, har izuwa cikin watan Nuwamba inda aka kona wani wurin cin abinci na wani iyalin Musulmai a Kansas. Hakan ya nuna karuwa a kan laifuka 260 da aka aikata a shekarar 2016
Kugniyar CAIR ta alakant karuwar laifukan tsano a kan Musulmi ne ga wasu manufofin shugaban Amurka Donald Trump musamman hana mutane daga kasashen da galibin al'umarta musulmi ne zuwa Amurka.


Da take maida martani ta sakon email, mai Magana da yawun fadar White House Kelly Love tace, gwamnatin Trump tana aiki ne da bin doka da oda kuma tana Allah wadai da duk wani nau'i na rashin bin doka ciki hara kyama ko tsanar mutane.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG