Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Nada Hannu a Boko Haram


 Abubakar Shekau shugaban Boko Haram
Abubakar Shekau shugaban Boko Haram

Duk yada aka so a fitar da gwamnatin taraiya daga cikin zargi,tana cikin zargi saboda da ita aka sani sojojin tane.

An zargi gwamnatin Najeriya da hannu a hare-haren da ‘yan boko haram ke kaiwa a arewacin Najeriya,inji shugaban mata marubutan Najeriya, Hafsat Ahmed Marshall a hiran da tayi da wakiliyar muryar Amurka Grace Alheri, ta wayan tarho.

Tace “duk yada aka so a fitar da gwamnatin taraiya daga cikin zargi,tana cikin zargi saboda da ita aka sani sojojin tane,sannan mutanenan tun abun nan bai kai haka ba, akace a neme su a sauna ayi sulhu dasu kamar yanda yayi da Niger Delta, ba abunda yayi akansu har abun nan yazo ya tabarbare."

"Saboda haka ko munaso ko bamuso dole a zargi gwamnatin taraiya da hannu a cikin abun nan da yake faruwa,ba yanda za’a yi ta fitar da kanta a cikin zargi."

Ta kara da cewa duk lokacin da aka yi kashe-kashen nan bata nuna damuwa ba ci gaba takeyi da harkanta,wasu na bada kwanaki ayi zamar makoki idan irin wadannan abubuwa sun faru kin taba ji Najeriya, ta bada ko yini daya,tace ayi zamar makoki wadanda suka mutu,saboda haka wannan abun dubawa ne.

Akan kwamitin da shugaban kasa ya kafa kanya binciki harkokin ‘yan boko haram cewa tayi babu wani abunda kwamiti zai yi,kwamiti nawa aka nada a Najeriya kin taba ganin kwamitin da aka nada aka ayi amfani da abunda kwamiti ya kawo.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG