A wani takaitaccen sako daya gabatar a jiya Laraba, shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana dalilansa na yanke shawarar janyewa daga takarar zaben bana, inda yace kare tsarin dimokradiyya ya fi kowane irin mukami mahimmanci”.
“Ina mutunta wannan mukami, sai dai na fi kaunar kasata. Mafi girman karimci a rayuwata shine zama shugaban kasarku. Amma akan batun kare tsarin dimokradiyya , wanda ke cikin wani hali, ina ganin hakan ya fi mahimmanci akan kowane irin mukami.
Ina samun kwarin gwiwa da jin dadin hidimtawa al’ummar Amurka. Amma wannan muhimmin aiki na kyautata hadin kan Amurka ya zarta muradan kashin kai na. Al’amari ne daya shafe ka da iayalan dama gobenku. al’amari ne daya shafemu a matsayin Al’umma.”
Ya kara da cewa, “a rayuwar aiki ana bukatar samun tsawon shekaru na gogewa. Haka kuma ana bukatar sabbin muryoyi, sabbin jini, muryoyin matasa”.
A cewarsa, “ana bukatar muryoyin matasa” inda ya kara da cewar “makomar amurka na hannunku.”
Shugaba Joe Biden ya janye daga takarar ci gaba da zama a fadar White House sannan a maimakon hakan ya bayyana goyon bayansa ga mataimakiyarsa, Kamala Harris.
Kamala harris na takarar zama mace ta farko da za ta kasance shugabar kasa a Amurka.
Dandalin Mu Tattauna