Yayin da take nanata goyon bayan Isra'ila na 'yancin kare kanta "daga Iran da mayakan da ke samun goyon bayan Iran din," da kuma yin Allah wadai da Hamas a matsayin "kungiyar ta'addanci," Harris ta yi kira da babbar murya akan a tsagaita wuta ba tare da bata lokaci ba.
"Kamar yadda na fada wa Firai Minista Netanyahu, lokaci ya yi da ya kamata a kulla yarjejeniyar tsagaita wuta," a cewar Harris a ranar Alhamis a yayin wani jawabi da ta yi bayan da ta dauki hoto da Netanyahu, inda ta yi magana gaba gadi amma cikin ladabi.
Kalaman da Harris ta yi sun sha bambam da na tsohon shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya dora alhakin rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya akan gwamnatin Biden, sannan ba tare ba da wata hujja ba, ya yi ikirarin cewa zai gaggauta warware rikicin Gaza idan aka zabe shi, abin da Trump ya fada wa manema labarai da suka tattaru a gidansa da ke jihar Florida kenan ranar Juma’a yayin da ya fara ganawa da Netanyahu.
A cewarsa "ya kyautata wa Isra'ila, fiye da duk wani shugaban kasa a Amurka," Trump ya bayyana manufofin goyon bayan Isra'ila da ya fidda a lokacin da ya yi wa'adin shugabancinsa na farko, ciki har da kulla yarjejeniyar Abraham da ta daidaita huldar diflomasiyyar Isra'ila da wasu kasashen Larabawa makwabtan, tare da mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Kudus da kuma amincewa da mamayar da Isra'ila ta yi wa tuddan Golan.
Dandalin Mu Tattauna