Yau take Sallah a daukacin kasashen musulmai a duniya, wadda ta yi dai dai da ranar juma’a. Dubban mutane a fadin duniya na murnanr wannan rana, kasancewar an kammala azumin wata mai albarka.
A Najeriya dai mutane a ko ina sun yi tururwa zuwa masallatai na idi domin gudanar da wannan ibada.
Wasu da muka samu zantawa da su a wurare da dama, sun bayyana mana cewar sun halarci masallacin idi, inda aka gudanar da sallah, kana kuma limamai sun yi jawabai masu dama da kuma ratsa jiki, inda su ka yi kira da mutane su sani cewar gama azumi ba shine karshen aikata ibadu ba.
Kada mutane su manta da cewar ibadun da suka gudanar a cikin wannan wata, da yagabata ibadune da yakamata ace sun cigaba da yin irinsu harma fiye, domin tahaka ne zasu samu rahamar Allah.
Malam. Aliyu Abdullahi Tekex, yayi karin haske dangane da falalar wannan rana, da irin abubuwan da ake bukatar ‘yan uwa musulmai su yi, ya ce akwai bukatar al’uma su yi ma kasar addu’ar zaman lafiya da ma dorewar tattalin azikin kasa, kana da yi ma shuwagabanni addu’oin neman Allah, ya ba su ikon aiwatar da mulkin su cikin adalci, domin kuwa idan ba mun yi masu addu’a ba to Allah, na iya jarabtar mu da wasu musifu.
Sai ya kara da cewar mutane su yi kokarin mikar da abubuwan da suka koya, a wannan wata na tausayi a kan marasa karfi, da hakuri, da duk wasu abubuwa da su ka san Allah, naso manzonsa ya yi koyi da a aiwatar wa.
A karshe ya yi kira ga mutane su ji tsoron Allah, su gudanar da bukin sallah lafiya cikin kwanciyar hankali da lumana, ya kuma kara jawo hankalin al’uma da su yi taka tsan-tsan da mugaye a cikin su, duk inda su ka ga mutun babba ko karami cikin wata suffa da basu yadda da ita ba, to su gaggauta sanar da hukumomi.