Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Da Shugaba Buhari Zai Kai Amurka


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na hanyar sa ta fara ziyarar aiki ta kwanaki hudu nan Amurka, inda zai gana da takwaran aikin sa da shugaba Amurka Barack Obama.

Rikicin Boko Haram zai kasance babban batun da shugabannin biyu zasu tattauna a fadar White House gobe Litinin in Allah ya kaimu.

Amurka na son fadada irin gudunmawar da take baiwa Najeriya a yaki da ‘yan bindigar, wadanda suka zafafa kai hare hare tun bayan kama aikin shugaba Buhari.

Shugabannin biyu ana sa ran zasu tattauna kan sauye sauyen da Najeriyar zata aiwatar ta fuskar siyasa da tattalin arzikin da zummar kawo karshen cin hanci da rashawa suka yiwa kasar katutu.

XS
SM
MD
LG