Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakon Barka Da Sallah Daga Mai Martaba Sarkin Musulmai.


Mai Alfarma sarkin Musulman Alhaji Mohammadu Sa'adu Abubakar ya gabatar da sakonsa na barka da Sallah ga daukacin musulman Najeriya da ma 'yan Najeriya baki daya, tun da a bana sakon nasa ya karkata ne ga kalubalen da kasar take ciki na rashin tsaro da tashe-tashen hankula.
Sai dai mai martaba ya lura cewa rashin ilimi na daya daga cikin musabbabin tashin hankalin. Kuma ya janyo hankalin shugabanni musamman a yankin arewa akan irin rata da aka yi wa arewa ta fannin ilimi, ya kuma ce ya kamata iyayaye su kai 'yayansu makaranta.
A bangaren tashe-tashen hakula kuma, mai martaba yace babu dalilin da zai sa 'yan Najeriya su dinga kashe junansu saboda bambance-bambancen da ke tsakanin su. Yana mai cewa dukan mu Allah ne ya yi mu kabilu dabam-dabam, da addinai dabam-bam, da Allah ya ga dama da sai yayi mu iri daya.

Mai martaba ya kara da yin kara kira ga 'yan Najeriya da su cigaba zaman lafiya tare da kyautata wa juna ba tare da nuna bambanci ba.

Ga sabbin shugabannin da aka zaba kuma ya ce ya zama wajibi a gaya masu gaskiya ba tare da tsoro ko fargaba ba.
Ga Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

XS
SM
MD
LG