Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harshe Da Karin Magana Tare Da Dr. Abdullahi Garba Imam


Dr. Abdullahi Garba Imam
Dr. Abdullahi Garba Imam

A shirin Harshe Da Karin Magana har yanzu muna tare da Dakta Abdullahi Garba Imam, na kwalejin Mallam Aminu Kano.

Zamu ci gaba ne da karin magana mai kambamawa, wanda Dakta ya bayyana shi a matsayin karin magana da ake amfani da shi mai nunin abin da aka fada ba mai yiwuwa bane, ko abu mai wahalar faruwa.

Dakta Abdullahi ya bayar da missalan ire-iren su kamar haka: “Wato abin mamaki mara lafiya yaci mara, shikuma mai lafiya yaci gutsire” idan aka duba dai an san cewa wannan lamari ba mai faruwa bane domin maras lafiya ba ya cin abinci mai yawa. “Ikon Allah Akuya ta cinye Kura” duk wanda yaji haka yasan hakan ba abune mai yiwuwa ba, sai dai Kura ta cinye Akuya.

Ire-iren wadan nan karin maganu na nan dayawa, wadanda ake cewa masu Kambamawa.

Saurari cikakkiyar hirar.

XS
SM
MD
LG