Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria Na Shirin Sake Amfani Da Makamai Masu Guba, in ji Amurka


Nikki Haley, Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya
Nikki Haley, Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya

Amurka ta zargi Syria da shirin sake yin amfani da makamai masu guba akan mutanen kasarta a wata sanarwa da ta fitar jiya Litinin da yamma, inda ta yi wa Syrian da kasashen Rasha da Iran masu goyon bayanta kashedi.

Fadar White House a Amurka ta ja kunnen shugaban Syria Bashar al- Assad akan shirin sake yin amfani da makamai masu guba da ya ke yi.

Amurka ta ce ta gano wasu shirye-shirye da ka iya kai ga mutuwar dubban mutane da za su hada da yara.

Sanarwar ta ce idan har Assad ya kuskura ya kai harin, shugaban da sojojinsa za su dandana kudarsu.

Can baya shugaban Amurka Donald Trump ya sa dakarunsa sun kai hari kan sansanin mayakan sojojin saman Syria bayan da Syria ta yi amfani da makamai masu guba a ranar 4 ga watan Afirilu wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 90 a yankin Idlib dake hannun ‘yan tawaye a lokacin.

Syria dai ta musanta zargin.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley a shafinta na Twitter ta ce duk wasu hare-hare akan jama’ar Syria za’a daurawa shugaba Bashsr al-Assad alhakinsu da Rasha da Iran, kasashe biyu da ake zargin marawa Assad baya wajen kashe al'umar kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG