Mr. Tillerson, wanda ya fidda sanarwa, kwana daya bayanda Qatar taki ta amince da sharuddan aka gindaya mata, tana mai cewa suna barzana ko taba diyaucinta, yace, "akwai sassa masu muhimmanci, da zasu iya zama shimfida na ci gaba da shawarwari da zasu kai ga cimma matsaya." Sakataren harkokin wajen na Amurka bai fadi kan wadanne batutuwa bane yake tunanin Masar, da hadaddiyar daular kasashen Larabawa, da Saudiyya zasu iya cimma matsaya da hukumomin na Qatar.
Kasashen Larabawan hudu, wadanna suka tsinka huldar difilomasiyya fiye da makonni biyu da suka wuce da Qatar kan zargin tana goyon bayan ta'addanci a yankin, a makon jiya ne ta hanun Kuwait mai shiga tsakani suka gabatar da sharuddansu, da suka hada da bukatar ta rufe tashar talibijin na al-Jazeera.
Facebook Forum