Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuka Sun Salwanta Sakamakon Hadarin Gocewar Kasa A kudancin China


Kyrgyzstan Osh Ozgon Ayu village landslide searches May 2, 2017
Kyrgyzstan Osh Ozgon Ayu village landslide searches May 2, 2017

A can kudu maso yammacin kasar China kuma, an fara fidda tsammani kan wasu mutane masu yawa da suka bace bayan wata mummunar gocewar kasa ko laka a yankin.

Jami'ai suka ce har yanzu akwai mutaen 93 da ba'a san inda suke ba, bayan da kasa mai yawan gaske ta binne kauyen da ake kira Xinmo a lardin Sichuan, al'amarin ya auku ne ranar Asabar. Jami'an lardin sunce gawarwakin da aka gano ba su kai 15 ba kamar yada aka yi bayani tun farko.
Har zuwa daren jiya Lahadi, mutane uku ne kadai aka ceto, wani magidanci da matarsa, da jariri dan wata daya, bayan da wani katon dutse da wasu baraguzai suka lalata gidaje akalla 40.
Mutane fiye da dubu uku ne, 'Yansanda da soja da farar hule ne suke aikin ceto, kamar yadda jamai'ai suka yi bayani. Masu aikin ceton suna aiki ba dare ba rana suna bi ta cikin baraguzan don ya-Allah su samu wani da ransa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG