Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Wa Wasu Jihohin Amurka Kutse A Yanar Gizo


Whatsapp
Whatsapp

Masu satar shiga internet, sun yiwa wasu jihohin Amurka dama-wasu kananan hukumoi kutse jiya Lahadi, inda suka wallafa sakonni dake nuna goyon baya ga kungiyar ISIS. "Hakkin duk jini da ake zubarwa a kasashen Musulmi yana wuyarka Trump kai da mutanenka, inji sakon. Sakon ya kare ne da cewa "Ina kaunar ISIS." Inda kutsen yafi tsanani shine a jahar Ohio, inda masu satar shiga rumbun internet din suka afkawa shafin gwamnan jahar John Kasich, da uwargidansa Karen Kasich, da shafin speto janar mai kula da sashen inshoran kiwon lafiya da ake kira Medicaid, da kuma na sashen fursina da ma wadansu. "Da zarar aka sanar da mu, muka fara daukar matakan gyara, muna ci gaba da sa ido, har sai an shawo kan lamarin baki daya," kamar yadda bayanai da ofishin gwamnan ya bayar suka nuna. Haka nan kutsen ya shafi karamar hukumar Howard a jahar Maryland da bashi da nisa da nan Washington, da kuma karamar hukumar da ake kira Brookhaven a jahar New York. Daga bisani a jiya Lahadin, an bude wasu shafukan da aka yiwa kutse, amma wasu da aka karya, har yanzu ba'a a sake bude su ba har zuwa asubahi nan agogon Amurka. Wata kungiya data kira kanta Team Systems DZ da turanci, ta dauki alhakin kai wannan kutse ko hari ta internet.

"Hakkin duk jini da ake zubarwa a kasashen Musulmi yana wuyarka Trump kai da mutanenka, inji sakon. Sakon ya kare ne da cewa "Ina kaunar ISIS."
Inda kutsen yafi tsanani shine a jahar Ohio, inda masu satar shiga rumbun internet din suka afkawa shafin gwamnan jahar John Kasich, da uwargidansa Karen Kasich, da shafin speto janar mai kula da sashen inshoran kiwon lafiya da ake kira Medicaid, da kuma na sashen fursina da ma wadansu.
"Da zarar aka sanar da mu, muka fara daukar matakan gyara, muna ci gaba da sa ido, har sai an shawo kan lamarin baki daya," kamar yadda bayanai da ofishin gwamnan ya bayar suka nuna.
Haka nan kutsen ya shafi karamar hukumar Howard a jahar Maryland da bashi da nisa da nan Washington, da kuma karamar hukumar da ake kira Brookhaven a jahar New York.
Daga bisani a jiya Lahadin, an bude wasu shafukan da aka yiwa kutse, amma wasu da aka karya, har yanzu ba'a a sake bude su ba har zuwa asubahi nan agogon Amurka.
Wata kungiya data kira kanta Team Systems DZ da turanci, ta dauki alhakin kai wannan kutse ko hari ta internet.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG