Firayim Ministar Birtaniya Theresa May ta ce tayin da tayi na kare hakkokin ‘yan wasu kasashen Turai dake zaune a Biritaniya bayan ficewar Birtaniyar daga kungiyar Tarayyar Turai, tayi ne bisa adalci da sanin ya kamata.
A lokacin da take jawabi a birnin Brussels, yini na biyu a taron kolin Tarayyar Turai, May ta ce “zuwa Litinin zamu fitar da ‘karin bayani kan shirye-shiryen.”
Sai dai kuma shugabannin kungiyar Tarayyar Turai basu yarda da cewa tayin da Birtaniya ta yi ya isa ba, inda suke cewa har yanzu akwai alamun tambaya a ‘kasa.
A jiya Alhamis ne shugaban kungiyar ke cewa dole ne su bi a hankali wajen shirye-shiryen ficewar Birtaniya daga kungiyar bayan da ta yanke hukuncin yin hakan, amma ya nemi hadin kai kan tattaunawar da za ayi nan gaba.
Shugabannin kungiyar Tarayyar Turan sun fara taron koli na kwanaki biyu a Brussels, domin tattaunawa kan batutuwa da suka hada da ficewar Birtaniya daga kungiyar da batun ta’addanci da bakin haure da dai sauransu.
Facebook Forum