Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Biyar A Jami’ar Tarayya Da Ke Garin Dutsin-Ma


MALI
MALI

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da sace dalibai mata biyar na jami'ar tarayya da ke Dutsin-Ma a jihar Katsina ranar Laraba a gidan da suke zama.

A cikin wata sanarwa da ya fidda, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Sadiq Aliyu Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Sadiq ya kuma ce an kama wani mutum da ake zargi da ba ‘yan bindiga bayanan sirri kana an kama wasu da dama da ake zagin suna da hannu wajen sata da yin garkuwa da daliban da akasarinsu mata ne. A halin yanzu dai an kaddamar da bincike don gano inda daliban suke da kuma ceto su a cewarsa.

Da misalin karfe biyu na safiyar Laraba ne dai wasu ‘yan bindiga suka kai samame a wani gida da daliban jami’ar tarraya ke haya a garin Dutin-Ma da ke jihar Katsina.

Jami’in watsa labaran jami’ar Malam Habibu ya tabbar da sace daliban, amma ya ce ba a cikin makaranta suke ba. Ya kara da cewa hukumar makarantar da jami’an tsaro suna kokarin ganin an kubuto da daliban.

Wannan dai na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da ‘yan bindiga suka sace daliban jami’ar tarayya da ke jihar Zamfara da ba'a tabbatar da adadinsu ba sannan a ‘yan kwanakin da suka gabata wasu ‘yan bindiga suka kutsa jami’ar Usman Dan Fodio da ke jihar Sokoto suka sace kayyan abinci.

Saurari cikakken rahoton Sani Shu’aibu Malumfashi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG