Manajan harkokin siyasa na gundumar Musawa Habibu Abdulkadir ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, wasu ‘yan bindiga da ke kan babura sun kai farmaki kauyen Kusa da ke gundumar Musawa da hatsin ranar Lahadi.
Ya ce sun bude wuta kan daliban da suke bikin Mauludi a tsakiyar kauyen, inda suka kashe 13 tare da raunata 20.
Ya ce jami’an ‘yan banga sun bazu a kauyen inda suka tunkari ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin daji.
Ya kara da cewa zuwan ‘yan banga ya hana maharan yin awon gaba da wasu daliban da ke wajen bikin.
Kakakin ‘yan sandan ya tabbatar da faruwar lamarin na Katsina amma ya ce mutane 18 ne suka jikkata a harin, inda biyu daga cikinsu suka rasu a asibiti.
‘Yan ta’addan da ke rike da sansanoni a manyan dazuzzukan da suka mamaye jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja, sun yi kaurin suna wajen sace dalibai da yawa a makarantu a shekarun baya.
~ AFP
Dandalin Mu Tattauna