Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga 11 Sun Ajiye Makamansu A Nijar


Wani jami'in tsaro yana karbar bindiga
Wani jami'in tsaro yana karbar bindiga

‘Yan bindiga a Nijar na cigaba da amsa kiran hukumomi kasar ta hanyar ajiye makamanai inda suke fitowa suna rungumar shirin zaman lafiya.

Makaman sun hada da harsashai masu yawa da kuma manyan bindigogi kirar AK47 da kuma kayayyakin yaki.

‘Yan bindiga fiye da goma ne suka mika makamansu ga mahukuntan jihar Agadas yau shekaru masu yawa da matasan suka shiga wannan aiki a iyakokin kasashen Algeria da libiya da kuma Nijar tare da jefa jama’a a cikin halin ha’hula’i.

‘Yan bindigar sun ce sun amsa kiran da shugaban kasar Muhammed Bazoum, ya yi musu ne a kan su ajiye makamai tare da kawo karshen miyagun dabi’un da suka runguma. Wadanda suka mika wuyar sun ce rashin aikin yi ne yasa suka shiga cikin ayyukan ta’addanci.

Wasu 'yan bindiga da suka ajiya makamansu
Wasu 'yan bindiga da suka ajiya makamansu

Hukumomi a Agadas dai sun yaba da yadda 'yan bindigar ke ajiye makamai domin rungumar zaman lafiya tare da bada hadin kai ga jami’an tsaro. Magaji Mamman Dada, gwamnan jihar Agadas yace;

"Zan isar da godiya ga wadannan 'yan bindigar da suka ajiye makamai saboda zaman lafiya bayan da shugaban Nijar yayi kira ga kungiyoyin da ke rike da makamai da su ajiye domin ciyar da kasa a gaba. Kun san tsaro shine ginshikin cigaban kowace kasa. Daga cikin makaman da suka ajiye akwai bindigogi kirar AK47 da nakoyoyi da kuma alburusai masu yawa. Muna kira ga sauran yan bindigar da suke rike da makamai da su zo su ajiye su domin rungumar zamaan lafiya."

A Nijar ‘yan bindiga 25 ne suka mika wuya wadanda mafi yawancin su matasa wadanda suka addabi mutane.a iyakokin kasar
A Nijar ‘yan bindiga 25 ne suka mika wuya wadanda mafi yawancin su matasa wadanda suka addabi mutane.a iyakokin kasar

Mohamed Abubakar dan kungiyar farar hula a Agadas na ganin wannan yunkurin na neman zaman lafiya abu ne mai kyau, to sai dai ya kyautu a sanya ido akan tubabbu yan bindigar.

'Yan bindigar sun dauki matakin dakatar da aikin na su domin a cewar su, karbar tayin zaman lafiya da shugaban kasar Nijar yayi musu da kuma wasu dalillai na daban.

~ Hamid Mahmoud

XS
SM
MD
LG