Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Nijar Goma Sun Mutu A Wani Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai 


Wasu 'yan bindiga
Wasu 'yan bindiga

Akalla sojojin Nijar goma ne aka kashe a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin kudu maso yammacin kasar da safiyar Alhamis, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro uku suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

An kai harin ne kimanin kilomita 190 (mil 118) daga Yamai babban birnin kasar a Kandadji, kusa da yankin kan iyakan Mali, Burkina Faso da Nijar, wanda ya kasance cibiyar 'yan tawayen ‘yan IS a yankin Sahel a cikin 'yan shekarun da suka gabata.

Majiyoyin da suka hada da wani babban jami’in soji da ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba su da izinin yin magana da manema labarai, ba su bayyana ko wace kungiya ce ke da alhakin hakan ba. Ƙungiyoyin cikin gida na al Qaeda da na IS suna aiki a yankin kuma suna kai hare-hare akai-akai kan sojoji da fararen hula.

Sojoji a jirage masu saukar angulu
Sojoji a jirage masu saukar angulu

Majiyoyin tsaro biyu sun ce sojojin sun mayar da martani kan harin da sojojin kasa da kuma jirage masu saukar angulu, wanda daya daga cikinsu ya samu rauni amma ya samu damar komawa sansaninsu.

Jamhuriyar Nijar dai na karkashin mulkin soji ne da ya kwace mulki a watan Yuli, wani bangare na nuna rashin jin dadinsa kan tabarbarewar tsaro. Kasashen Mali da Burkina Faso da ke makwabtaka da kasar sun yi juyin mulki sau biyu a cikin shekaru uku da suka wuce.

Sai dai kuma masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce an sha fama da hare-hare a jamhuriyar Nijar karkashin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, wanda ya yi yunkurin dakile aiyukan ‘yan ta’adda da kuma yankunan karkara inda suka samo asali.

Akalla sojoji 17 ne aka kashe a wani harin da aka kai a kudu maso yammacin Nijar a tsakiyar watan Agusta.

Faransa ta ce a ranar Lahadin da ta gabata za ta janye sojojinta 1,500 daga Jamhuriyar Nijar kafin karshen wannan shekara, bayan shafe makwanni suna samun matsin lamba daga gwamnatin mulkin soji da kuma zanga-zangar adawa kan mulkin mallaka daga magoyan bayan sojojin juyin mulkin, wanda ke da dakaru a can don yakar masu tada kayar bayan.

A ranar Alhamis din da ta gabata daruruwan magoya bayan gwamnatin Junta ne suka sake taruwa a gaban sansanin sojin Faransa da ke Yamai babban birnin kasar domin neman sojojin su fice.

~ REUTERS

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG