Rahotanni daga Najeriya na cewa sojojin kasar sun kutsa kai cikin dajin Sambisa da ke jihar Borno, dajin da ake mai kallon mafaka ce ga ‘yan kungiyar Boko Haram masu ta da kayar baya.
Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar dauke da sa hanun darektan hulda da jama’a, Manjo Janar Chris Olukolade, ta bayya cewa sojojin sun samu sun kakkabe duk abin da ke cikin dajin.
“Sun samu kutsawa cikin wannan daji a wani kauye da ake kira Alagarno, wannan kauye a karamar hukumar Damboa ya ke, kuma a cewar sanarwa an yi arangama da mayakan Boko Haram har an samu asarar rayuka ma.” In ji wakilin Murayar Amurka Haruna Dauda dake Maiduguri.
Rundunar dai ba ta bayyana adadin mutanen da suka mutu ko kuma ko mamatan sun hada har da sojoji ba, sai dai sanarwar ta ce sojojin sun kwato makamai da dama ciki har da tankunan yaki da mayakan suka kwace a hanun dakarun Najeriya.
Wakilin Muryar Amurka ya ce babu tabbacin aukuwar wannan lamari amma rundunar sojin ta hada sanarwar tare da wasu hotunan kayayyakin da suka yi ikrarin sun kwato daga mayakan.
Ga karin bayani a tattaunawar Usman Ahmad Kabara da wakilinmu Haruna Dauda da ke Maiduguri.