Wakilinmu Haruna Dauda Biu ne ya sanar da Muryar Amurka a hirarsa da Usman Kabara a yau Juma’a 27 ga watan Maris din shekarar nan ta 2015.
Haruna yace su ‘yan jarida sun sami wata sanarwa da sojojin Najeriya suka fitar ta hannun kakakinsu Manjo Janar Chris Olukolade da suka ce sun fatattaki ‘yan boko haram inda wasu suka mutu wasu kuma suka tsere daga garin zuwa makwabta kamar su Kamaru da Chadi.
Sanarwa ta fito tare da hotunan da ke nuna cewa sun kwace garin daga hannun ‘yan ta’addar. Wakilinmu ya fada mana a cikin hotunan akwai wadanda suka nuna wata tankar yaki da a da ‘yan boko haram suke amfani da ita har ma sun sha nunata a faya-fayen bidiyonsu da suke wurgawa a shafinta na YouTube a yanar gizo.
Sai dai sojojin ba su nuna an rasa rayukan jama’ar garin Gwoza ba ko a’a lokacin da ake fafata fadan ba. Olukolade ya nuna cewa Gwoza ne gari na karshe a wanda ake mallake da su kuma sun kwato shi yau. Amma rahotanni sun nuna cewa har yanzu garuruwan Kalabargi da Abadam na karkashin ikon mayakan na boko haram.
Sojojin sun tabbatar da cewa ba zasu bar ragowar ‘yan boko haram din da suka tsere zuwa makwabtan Najeriya ba da suka sha wuta. Sun ce zasu ci gaba da farautarsu har sai sun ga abinda ya turewa buzu nadi. Jama’ar garin Gwoza dai na murna da wannan nasara in wakilin namu.