Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Ina Abubakar Shekau Madugun Boko Haram Yake


Abubakar Shekau (File Photo)
Abubakar Shekau (File Photo)

Duk alkawuran da shugaban kasar Najeriya yayi akan Boko Haram da yawa bai cikasu ba sai kuma gashi yace za'a kwato Gwoza yau Juma'a.

Alkawarin da shugaban kasar Najeriya yayi na cewa zai kama Abubakar Shekau kafin zaben da za'a fara gobe bai cika ba. To ko menene dalili?

Yanzu shugaba Jonathan ya sake yin wani alkawarin cewa za'a kwato Gwoza daga hannun 'yan Boko Haram yau din nan, wai domin a tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a duk fadin arewa maso gabas da kasar gaba daya. Idan ba'a manta ba rashin tsaro ya addabi arewa maso gabas na har tsawon shekaru shida.

Shugaban Najeriya yayi wannan sabon alkawarin ne lokacin da yake karbar bakuncin wasu daga tarayyar turai da suka zo sa ido a zabukan da za'a yi. Ya kara da cewa an yiwa 'yan Boko Haram kafar rago kuma an karya masu lago yadda ba zasu iya yiwa zaben kasar barazana ba.

Wani mai fashin baki Malam Husseini Mongunu dake zaune a Miduguri jihar Borno, jihar da 'yan Boko Haram suka yi kakagida, yace alkawarin da shugaban kasa yayi magana ce irin ta 'yan siyasa. Duk lokacin da dan siyasa yake neman wani abu zai iya fadan abun da mutane ke son ji. Yace 'yan Boko Haram sun dade a Gwoza sabili da haka karbe garin a hannunsu zai yi wuya.

Mongunu yace sojojin Nijar da Chadi na iya cafke garin to amma sojojin Najeriya da kyar su yadda su shiga garin. Yayi misali da garin Damasak da sojojin Chadi da Kamaru suka kwato amma domin sojojin Najeriya sun ki shiga garin yanzu ya koma hannun 'yan Boko Haram. Yace a tsarin sojoji duk garin da aka kwato yakamata sojoji su kasance a garin domin su cigaba da yin shara, wato su gano nakiyoyi kuma su ciresu.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG