Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekau Yana Gwoza-Inji Wasu Mata Da Suka Kubuta


 Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram.
Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram.

Munyi kwanaki muna cikin jeji, mu buya da rana, mu tafi cikin dare.

Daya daga cikin mata su kamar tara da suka tsere daga hanun Boko Haram tace Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram yana Gwoza, ta ganshi da idanunta, kuma ko yanzu ta ganshi zata ganeshi.

Wannan mata wacce bata bayyana sunanta ba, tace shekarunta 38, kuma tana da 'yaya bakwai. Tace wata uku suna hanun 'yan kungiyar ta Boko Haram kamin su tsere.

Malamar tace sun gudu ne sakamakon wani makami da aka harba kan garin na Gwoza, al'amarin da ya tilastawa suma 'yan binidgar ranta cikin na kare.

Suka fito Gulak, suka hadu da 'yan banga wadanda suka mika su ga sojoji. Anan ta ci gaba da bayanin cewa, sojojin suka yiwa wasu daga cikinsu da basu da koshin lafiya jinya, sannan daga bisani tareda taimakon Boni Haruna, Minista kuma tsohon Gwamnan jihar Adamawa, aka kai su Maiduguri, babban birnin jihar Barno.

Ga karin bayani.

Shekau Yana Gwoza-Inji Wasu Mata Da Suka Kubuta - 2'35"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG