Sojojin kasar Chadi sun ce sun gano gawarwakin sama da mutane dari a wani makeken kabari a garin Damasak na Najeriya bayanda suka taimaka aka kwato kauyen daga mayakan Boko Haram.
Sojojin sun ce an yiwa wadansu mutanen yankan rago. Sun ce an sami makeken kabarin ne a karkashin wata gada dake bayan garin.
Shaidu sun ce bisa ga ganin yanayin da gawarwakin yake ya nuna cewa an jima da kashe su.
Kungiyar Boko Haram ta kwace garin Damasak dake kusa da kan iyaka da Nijar cikin watan Nuwamba, sai dai dakarun Jamhuriyar Nijar da Chadi sun kwato garin kwanan nan a yunkurin hadin guiwa na murkushe mayakan.
Kungiyar Boko Haram ta shafe shekaru shida tana kai hare hare a arewacin Najeriya, da ya yi sanadin kashe dubban mutane,sama da miliyan daya kuma suka kauracewa matsugunansu.
Bayanda kungiyar ta fadada kai hare harenta kasashen dake makwabta da Najeriya, kasashen suka hada hannu da Najeriya wajen kai farmaki da ya kai ga kwato wadansu garuruwan dake arewa maso gabashin Najeriya cikin wata guda da ya shige.
Tun farko cikin wannan makon, kungiyar Boko Haram ta kashe a kalla mutane goma a garin Gomboru,abinda ya nuna cewa, zasu iya ci gaba da kai hare hare duk da tilasta masu ja da baya.