Zasu fara atisahin ne daga kasar Ghana zuwa Najeriya da Kamaru kana su karkare a Gabon.
Real Admiral Jonathan Ango shi zai jagoranci mayakan ruwan Najeriya a wajen atisahin. Yayinda yake shaidawa manema labarai yace bangaren dake kula da nahiyar Afirka na dakarun Amurka shi yake daukan nauyin shirya atisahin kowace shekara.
A wannan shekarar zasu fara ne daga kasar Ghana kafin su karkare a kasar Gabon bayan sun ratsa cikin ruwayen Najeriya da Kamaru. Wadanda zasu yi atisahin sun hada da kasashen Angola, Spain da Birtaniya da Jamus da dai sauransu.
Real Admiral Jonathan Ango ya bayyana alfanun atisahin. Yace atisahin yana koya masu yadda zasu hana barayin kan teku musamman masu satar mai samun nasarar ayyukan asha da su keyi.
Akwai wasu hukumomin Najeriya da zasu shiga atisahin kamar hukumar kwastan da na shige da fice da masu yaki da miyagun kwayoyi da dai wasu.
Ga rahoton Umar Hassan Tambuwal.