A farkon wannan makon ne tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu Thabo Mbeki ya kai ziyara Najeriya, har ya gana da shugaban kasa Goodluck Jonathan, da kuma babban abokin hamayyarsa Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.
Saura sun hada da tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, da kuma shugaban hukumar zabe Farfessa Attahiru Jega.
Kodashike ganawar cikin sirri aka gudanar, masu lura da al'amuran yau da kullum sun ce hakan ba zai rasa nasaba da kokarin karfafa tsarin Demokuradiyya, ta wajen ganin an gudanar da zabe kamar yadda aka shirya, kuma a kaucewa tarzoma, tareda tabbatar da cewa duk wanda ya sami nasara a zaben, a mutunta burin jama'a.
Wani masani da ya taba shugabantar cibiyar raya Demokuradiyya a Abuja, Dr Jibril Ibrahim, ya gayawa Umar Farouk Musa, cewa, irin wannan ziyara tana tasiri, ganin rawar da tsohon Magatakardan MDD Kofi Annan yayi a zaben da aka gudanar a Kenya a baya bayan nan.
Ga karin bayani.