Wani samame da sojan kundumbalan Amurka suka kai ya sa aka kwato wadansu ma’aikatan bada agaji guda biyu – daya wata macce ‘yar Amurka da kuma namiji dan kasar Denmark – wadanda ‘yan bindigar Somalia suka sace tun kamar makkoni ukku da suka gabata.
A cikin jawabin da ya yiwa kasa jiya, shugaba Barack Obama ya jinjinawa wannan yunkurin na sojan, wanda a lokacinsa suka fito da Jessica Buchanan da Poul hagen Thisted, wanda ke aiki da wata cibiya ta kasar Denmark dake aikin bada agaji na kawarda nakiyoyin da akan bizne a kasashen da ake rikici a cikinsu a Afrika da Gabas ta Tsakiya.
A cikin watan Oktoban bara ne aka sace su a garin Galkoyo na tsakiyar Somalia din. Cibiyar da suke yiwa aiki tace yanzu haka dai an kai su wata ma’ajiyar sirri an ajiye, kuma ko kwalzane basu samu ba na rauni.