Sojojin kasar Masar sun girka kansu tsakanin masu zanga-zangar goyon baya da na kin jinin gwamnati a babban birnin kasar, inda aka fara harbe harbe da safiyar yau Alhamis bayan wata mummunan arangama tsakanin bangarorin biyu. An girke tankokin yaki da dama daura da Dandalin Tahir, yayinda dubban masu zanga-zangar kin gwamnati ke taruwa suna kafa shingaye. Daya daga cikin tankokin na girke ne a wata babbar hanyar da ke sama, inda dazu da safe magoya bayan Shugaba Hosni Mubarak su ka yi ta jefo duwatsu kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da ke can kasa. Kafofin yada labarai sun ce shaidun gani da ido sun ce akalla mutane hudu sun mutu a tashin hankali na baya bayan nan. Sojoji sun kama mutane da dama a wurin, to amma babu bayanin ko su waye aka kama. Dan gwagwarmayar tabbatar da damokaradiyya Mohammed Elbaradei ya shaidawa tashar BBC cewa gwamnati na amfani da dabarar “firgitarwa” ya kuma ce yana ganin arangamar ka iya zama jina-jina.
Sojojin Misra sun girka kansu tsakanin masu zanga-zangar goyon baya da na kin gwamnati a babban birnin kasar.