Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iya mai mulkin kasar yau asabar, yayinda dubban masu zanga zangar kin jinin gwamnati ke ci gaba da gangami a dandalin ‘yanci suna kira gare shi da ya yi murabus a matsayin shugaban kasa. Tashar talabijin da kasar Masar tace shugabannin jam’iyar National Democratic baki daya sun yi murabus. Rahoton ya kuma bayyana cewa, dan shugaban kasar, Gamal Mubarak yana daga cikin wadanda suka sauka daga mukamansu a jam’iyar. Jam’iyar ce ke shugabanci a kasar kuma ta janyo kakkausar suka daga al’ummar kasa da kasa dangane da zaben majalisa da aka gudanar bara wanda jam’iyun hamayya suka ce an tafka magudi.
Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iya mai mulkin kasar yau asabar.