Dubban masu zanga zanga a dandalin ‘yanci na Tahrir dake birnin Alkahira sun shafe kwanaki goma sha biyu suna zanga zangar kin jinin shugaba Hosni Mubarak wanda ya shafe shekaru talatin bisa karagar mulki. An ji karar bindiga da asubahin yau a dandalin, sai dai babu rahoton wadanda suka jikkata. Kafar sadarwar kasar Masar ta laburta cewa, Mr. Mubarak ya gana yau asabar da manyan jami’an harkokin tattalin arzikin kasar, da suka hada da membobin sabuwar majalisar zartaswarsa da dama, domin tattaunawa kan rudamin, da yake janyowa kasar asarar dala miliyan dari uku da goma kowacce rana. Jiya jumma’a dubun dubatan masu zanga zangar kin jinin gwamnati suka yi cincirindo a dandalin Tahrir domin abinda suka kira “ranar ficewar” Mr. Mubarak wanda ya ci alwashin kamala wa’adin mulkinsa. Shugaban kungiyar hadin kan larabawa, Amr Moussa ya shiga sahun masu zanga zangar a dandalin jiya jumma’a. Dadadden jigon siyasa a kasar Masar din yace ya yiwu ya tsaya takarar shugaban kasa. Ministan tsaron kasar Hussein Tantawi shima ya ziyarci dandalin jiya. An kuma sami rahotannin arangama da kuma harbi a iska jiya jumma’a, yayinda jami’an soji suka hana wata kungiyar magoya bayan Mubarak shiga dandalin Tahrir. Masu zanga zangar sun yi nasu gangami a wani wuri dabam wanda suka kira, “Ranar nuna biyayya.”
Shugaba Hosni Mubarak ya gana da manyan jami’an harkokin tattalin arzikin kasar, da suka hada da membobin sabuwar majalisar zartaswarsa da dama, domin tattaunawa kan rudamin, da yake janyowa kasar asarar miliyoyin dala kowacce rana.