Dimbin ‘yan jaridar kasashen waje masu aika labarin boren da jama’a ke yi a kasar Masar,sun sha duka da hare-hare a hannun masu zanga-zangar goyon bayan gwamnatin kasar, a cikin wani al’amarin da ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta bayyana da cewa, da ma wani shiri ne aka tsara da niyyar razana kafofin yada labaran kasashen waje.
Haka kuma a ranakun Laraba da alhamis, jami’an tsaron kasar Masar sun kama dimbin ‘yan jarida a cikin su har da wakilan jaridun Amurka na New York Times da Washington Post, da kuma na gidan talbijin din AlJazeera mai cibiya a kasar Qatar. Amma dukkanin ofisoshin su ukku sun ce an sake su.
Dimbin cibiyoyin yada labarai da su ka hada da BBC, ABC News, da Swiss TV, dukan su sun bada labarin cewa an kaiwa ma’aikatan su hare-hare a cikin tarzomar da ta barke a tsakiyar birnin AlKahira tsakanin magoya bayan shugaba Hosni Mubarak da kuma masu zanga-zangar nuna kyamar gwamnati wadanda su ka dage lallai sai sun tursasa mi shi yin murabus daga mulki.
Kungiyoyin kare hakkokin bil Adama sun ce an kama ‘yan gwagwarmaya kamar talatin da su ka hada da ‘yan kasar Masar da kuma ‘yan kasashen waje, a jiya alhamis a yayin wata dirar mikiyar da jami’an tsaron musamman su ka yi a cibiyar Hisham Mubarak ta lauyoyi a birnin AlKahira .
‘Yan jarida sun ce, cikin hasala magoya bayan Mr.Mubarak su ka kai mu su hari saboda a ganin su kafofin yada labaran kasashen waje na goyon bayan masu zanga-zangar nuna kyamar gwamnati. Gwamnatin kasar Masar ta zargi kafofin yada labaran da goyon bayan masu zanga-zangar neman lallai Mr.Mubarak ya yi murabus maimakon ba shi damar kammala wa’adin mulkin shi.
A jiya alhamis sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta yi wata zazzafar suka game da hare-haren da ake kaiwa masu zanga-zanga cikin lumana, da ‘yan rajin kare hakkokin bil Adama da ‘yan kasashen waje da kuma jami’an diflomasiya.