WASHINGTON, D. C. - Sun bayyana cewa, hare-haren da sojojin suka kai sun hada da wuraren hada kayan aiki, na’urorin kare makamai da ake harbawa ta sararin sama, da wuraren ajiyar makamai, da kuma wuraren harba makamai.
Shugaba Joe Biden ya ce an kai hare-haren ne don nuna cewa, Amurka da kawayenta "ba za su lamunci" hare-haren da kungiyar 'yan ta'addan ke kai wa a tekun Bahar Rum ba. Kuma ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan da suka yi yunkurin yin shawarwarin diflomasiyya da kuma kyakkyawan nazari.
"Wadannan hare-haren suna mayar da martani kai tsaye ga hare-haren Houthi da ba a taba gani ba a kan jiragen ruwa na kasa da kasa a cikin tekun Bahar Maliya, ciki har da yin amfani da makami mai linzami karo na farko a tarihi," in ji Biden a cikin wata sanarwa.
Ya yi nuni da cewa, hare-haren na jefa jami’an Amurka cikin hadari, ma’aikatan ruwa na farar hula da kuma kasuwanci da ke fuskantar barazana, ya kuma kara da cewa, “Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen daukar wasu matakai don kare jama’armu da gudanar da harkokin kasuwanci cikin ‘yanci kamar yadda ya kamata”.
Hare-haren sun zama martanin farko da sojojin Amurka suka yi kan wani harin da jiragen yakin Isra'ila da Hamas suka yi na ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa marasa matuka da makamai masu linzami.
Hare-haren na soji na zuwa ne mako guda bayan da fadar White House da kuma wasu kasashen da ke kawance da su suka yi gargadin karshe ga Houthis da su daina kai hare-hare ko kuma su fuskanci matakin soji.
Jami’an sun bayyana harin a bisa sharadin sakaya sunansu dangane da bayani a kan abinda ya shafi ayyukan sojoji. A ranar Alhamis din da ta gabata ne ‘yan Majalisar Dokokin Amurka suka sanar da shirinkai harin.
-AP
Dandalin Mu Tattauna