Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Rushe Gwamnati a Burkina Faso


Sojoji su na kokarin hana 'yan zanga-zanga isa ginin majalisar dokoki a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso, Oct. 30, 2014.
Sojoji su na kokarin hana 'yan zanga-zanga isa ginin majalisar dokoki a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso, Oct. 30, 2014.

Babban kwamandan sojojin kasar Burkina Faso, Janar Honoré Traoré, ya bayarda sanarwar rushe majalisar dokoki.

Babban kwamandan sojojin kasar Burkina Faso, Janar Honoré Traoré, ya bayarda sanarwar rushe majalisar dokoki, tare da kafa gwamnatin rikon kwarya wadda zata jagoranci kasar na tsawon watanni 12.

Amma kuma Janar Traoré bai bayyana ko wanene zai jagoranci sabuwar gwamnatin ba.

Sanarwar babban hafsan sojojin ta zo jim kadan a bayan da shugaba Blaise Compaoré ya bada wata sanarwar da aka karanta a gidan rediyon Omega FM, yana fadin cewa ya rushe gwamnati, ya kuma ayyana kafa dokar-ta-baci a fadin kasar, matakan da babban hafsan sojojin kasar ne zai aiwatar da su.

Janar Traore ya fadawa wani taron 'yan jarida a Ouagadougou, cewa "Za a kafa hukumar mulkin rikon kwarya ta hanyar tuntubar dukkan jam'iyyu da bangarori. Ana sa ran maido da yin aiki da tsarin mulki a cikin watannin da ba zasu shige 12 ba."

Har ila yau ya ayyana kafa dokar hana mutane fita waje daga karfe 7 na maraice zuwa karfe 6 na safiya a duk fadin kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG